Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Kama Masu Safarar Makamai A Filato


Wasu daga cikin makaman da aka kama (Hoto: Facebook/Rundunar sojin Najeriya)
Wasu daga cikin makaman da aka kama (Hoto: Facebook/Rundunar sojin Najeriya)

Wata sanarwa da Kakakin rundunar Manjo Stephen Nantip Zhakom ya fitar a ranar Talata ta ce an kama makaman ne a wani same da aka kai a karamar hukumar Jos ta arewa a jihar.

Rundunar wanzar da zaman lafiya a jihar Filaton Najeriya ta Operation Safe Haven ta kama wasu fitattun masu safarar makamai guda 5 tare da kwace makamai da alburusai a wani gagarumin aikin leken asiri da aka gudanar a Jihar.

Wata sanarwa da Kakakin rundunar Manjo Stephen Nantip Zhakom ya fitar a ranar Talata ta ce an kama makaman ne a wani same da aka kai a karamar hukumar Jos ta arewa a jihar.

“An fara wannan aiki daga tsakiyar daren ranar 16 ga Satumba, 2024 zuwa safiyar ranar 17 ga Satumba, 2024.

Sojojin sun kai samame a mafakar wani mai safarar makamai da aka gano da suna Mohammed Sani a Yankin Ma'adinan Naraguta a Bayameni kusa da Bauchi Road a Karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, inda aka kama wanda ake zargi da wasu mutane 4.” Sanarwar ta ce.

Ta kara da cewa an kuma kwace makamai da alburusai iri-iri kamar yadda aka jera a kasa:

a. Bindigogi AK-47 guda biyu.
b. Bindiga Fabrique Nationale ta atomatik guda daya.
c. Kurtun AK-47 guda goma sha hudu.
d. Mujallar Fabrique Nationale guda daya.
e. Alburusai 5,316 na 7.62 MM (Special).
f. Alburusai casa'in da takwas na 7.62 MM (NATO).
g. Alburusai 43 na 9 MM.

"A halin yanzu ana yi wa wadanda ake zargin tambayoyi don samun bayanan sirri masu amfani da za su taimaka wajen cafke sauran mambobin kungiyar da kuma rushe tsarin samar da makamai." Manjo Zhakom ya kara da cewa.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG