Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Filato: 'Yan Sanda Sun Kama Mutum Sama Da 50 Da Ake Zargi Da Ta Da Husuma A Lokacin Zanga-zanga


Lokacin da aka
Lokacin da aka

Rundunar 'yan sandan jihar Filato da ke tsakiyar arewacin Najeriya ta kama mutum 51, da take zargi da haddasa rikici a garin Jos, wanda ya kai ga sace dukiyoyin jama'a da daga tutocin kasar Rasha.

Wadanda rundunar ta kama dai sun hada da matasa da yara kanana masu shekaru kasa da 15, wanda kuma tuni ta tisa keyarsu zuwa kotu, yayin da kotun ta umurci a tsaresu a gidan gyara hali, don ci gaba da shara'a.

Khadimullah Zakariyya, mai shekaru 16, 'yan sandan sun zarge shi ne da daukar tutar kasar Rasha.

Wasu matasa da ake zargi da ta da rikici a lokacin zanga-zanga a jihar Filato
Wasu matasa da ake zargi da ta da rikici a lokacin zanga-zanga a jihar Filato

Wani yaro kuma mai shekaru 10 da 'yan sandan suka kama cikin wadanda ke satar dukiyar jama'a ya ce ya gano wani da ke raba wa yara kudi don su shiga zanga-zangar ne.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Filato, DSP Alfred Alabo ya gargadi bata-gari da su guji aikata barna a jihar, domin hukuma ba za a kyalesu hakan nan ba.

Matasan da 'yan sanda suka kama a lokacin zanga-zanga A Jos, Jihar Filato
Matasan da 'yan sanda suka kama a lokacin zanga-zanga A Jos, Jihar Filato

Jami'in hulda da jama'a da gwamnan jihar Filato a Jos ta Arewan-Arewa, Nura Shehu ya ce sun yi mitin da masu ruwa da tsaki don tabbatar da zaman lafiya a garin na Jos.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto dai, dokar hana fita na aiki a garin Jos, daga karfe shida na yamma zuwa karfe goma sha biyu na rana.

Saurari cikakken rahoto daga Zainab Babaji:

Filato: 'Yan Sanda Sun Kama Mutum Sama Da 50 Da Ake Zargi Da Ta Da Husuma A Lokacin Zanga-zanga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG