Jami’an addinan biyu na magana ne a shirye-shiryen da su ke jagoranta na kawo fahimtar juna tsakanin Musulmi da Kirista da wasunsu, su ka samu sabani sanadiyyar lamuran siyasa.
Nuraini Ashafa da Movel Wuye wadanda su ka taba samun raunuka sanadiyyar rikicin addini sun ce bisa ga tanadin tsarin mulki, kowa ya na iya bin addinin da ya ga zai fishsheshi ba tare da samun tsangwama ba.
Sheikh Ashafa ya ce matukar za a rika zama tare to za a iya samun maslaha ga kowace irin fitina ko kiyayya a tsakanin jama’a.
A nasa bangare, Pastor Movel Wuye, ya ce ta hanyar dabi’u masu kyau da kyautatawa tsakanin mabiya addinai za a samu fahimtar juna da zaman da ya sabawa na doya da manja.
Wasu malaman addini a bangaren Musulmi da Kirista na amfani da damar bayan babban zaben Najeriya wajen jan hankalin mabiya addinan da ko sun yi zabe bisa shaukin addini, to yanzu lokacin ci gaba da zaman tare ne a kasa daya mai addinai, kabilu daban-daban da ra’ayoyi da kan ci karo da juna.
Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-hikaya:
Your browser doesn’t support HTML5