Xiaomi Ya Kirkiri Wayar Da Zata Maye Gurbin Galaxy Note 7

Ga mutanen da suke matukar so su mallaki wayar Samsung Note 7 amma yanzu babu hali saboda an dakatar da sayarwa da kuma sarrafasu, kafanin Xiaomi ya samar da mafita ta hanyar kera wayar Mi Note 2.

Kamfanin Xiaomi ya fitar da sanarwar fitar da sabuwar wayar da ya kera a birnin Beijing na kasar China, wayar dai na kama da wayar Note 7 ta hanyoyi da dama.

Duk da cewar wayar Mi Note 2 ba kawai tayi kama da sabuwar wayar Samsung bane ta ido, amma duk wasu abubuwa da wayar ke kunshe da su sun kusa zuwa dai dai da na wayar Mi Note 2, wata fasahar da Note 2 ke dauke da ita ta wuce ta Galaxy Note 7.

Wayar Note 2 samfurin 64 gigabyte tana da RAM mai girman gigabyte 4, ita kuma samfurin 128 gigabyte tana da RAM mai girman gigabyte 6. Idan kuma aka kwatanta da wayar Note 7 wadda ke da samufurin 64 gigabyte tana da gigabyte 4 ne kadai.

Wannan waya da kamfanin China ya kera tana da Kyamara daukar hoto mai girma wadda ta wuce ta Note 7, domin tana da megapixel 22.5 na’urar daukar hoto dake a bayan wayar, sai kuma wadda ke da megapixel 8 a na’urar dake fuskar wayar. Idan aka kwatanta ta da ta wayar Samsung wadda take da megapixel 12 kacal, sai kuma na’urar gaban wayar mai megapixel 5.

Baki daya wayoyin suna da batirin lithium-ion, amma batirin wayar Note 2 da alama yafi na Samsung tun da shi baya kamawa da wuta.

Wayoyin kamfanin Xiaomi dai na karbuwa a kasuwar Afirka, sai babu masaniyar ko ya wannan waya zata karbu ga kasashen, idan aka kwatanta da wayoyin da kamfanin ya sayar a baya tabbas akwai kyakkyawan zato wayar zata karbu.

Your browser doesn’t support HTML5

Xiaomi Ya Kirkiri Wayar Da Zata Maye Gurbin Galaxy Note 7 - 1'51"