Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Zumunta Na "Twitter" Na Shirin Rage Ma'aikata 300!


Kamfanin Twitter
Kamfanin Twitter

Shahararren kamfanin sadarwa na yanar gizo, “Twitter” na shirye shiryen rage ma’aikatan su da kashi takwas 8%. Kimanin ma’aikata dari uku 300 ke nan. Hakan kuwa yazo ne a dalilin rashin masu siyan kamfanin biyo bayan faduwar hannun jarin kamfanin.

Wannan zai iya zama karo na biyu da kamfanin yayi irin wannan sallamar ma’aikatan, a shekarar da ta gabata lokacin da sabon shugaban kamfanin ya dauki ragamar aiki Mr. Jack Dorsey, ya rage ma’aika kusan dari uku 300.

Zuwa yanzu dai hukumomin kamfanin ba suyi magana ba, dangane da matsalar, amma a yau ake sa ran kamfanin zasu fitar da rahoton su na tsakiyar shekara, wanda ana saran, za suyi karin bayani. Hannun jarin kamfanin dai sun fadi da kaso arba’in 40% a cikin shekara daya.

A watan Mayu da ya gabata ne kamfanin ya cika shekara goma 10, da kafuwa, amma har ya zuwa yau, basu gabatar da ribar da suka samu ba. Kamfanin dai sunyi wani sabon garon bawul ga shafin nasu, wanda yanzu haka mutun zai iya rubutu da ya kai yawan haruffa dari da arba’in 140.

Duk dai da cewar kamfanin, yana fuskantar barazana daga kamfanin zumunta na Facebook da Snapchat. Hannun jarin kamfanin ya sauka da kaso biyar 5%.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG