Facebook ya kaddamar da wata manhaja mai suna Lifestage domin janyo hankulan yara da matasa, ta yadda zasu dauka sabuwar manhajarta ta fi ta SnapChat.
Sabuwar manhajar da yanzu haka ana iya samunta ne akan manhajar Apple ta iOS, wadda kuma ake sa ran nan bada dadewa ba za fitar da wadda zata iya aiki akan manhajar Android. Ita dai wannan app ta Lifestage, ta kasance kamar wata ma’ajiyace ta hotunan bidiyo inda mutum zai iya amsa wasu tambayoyin tarihin kansa.
Maimakon mutum ya rubuta amsar tambayoyin sai ya ‘dauki kansa wani karamin hotan bidiyo da sauran mutane zasu iya kalla a shafinsa. Kuma duk lokacin da wani ya sabunta shafinsa, zai tallatawa sauran mutane da su duba canjin da akayi. An dai kirkiri wannan manhaja domin kananan yara masu ‘kasa da shekaru 21 da haihuwa, amma idan mutum ya wuce wannan shekarun ba zai iya ganin shafin wasu ba sai nashi kadai, kuma ba zai iya yiwa kowa magana ba.
Ga masu amfani da wannan app zasu iya zabar makarantar da suke, amma ba zasu iya ganin kowa ba har sai mutane daga makarantar har 20 sun fara amfani da ita.
Sai dai kuma babu tabbacin yadda app din zata hana mutanen da shekarunsu ya haura 21 wajen amfani da ita. Sai dai tana da ka’idar barin mutum a makaranta daya tal da yayi rijistar ta, ba tare da ya canza ba. haka kuma tana da wasu fasaloli da zasu iya taimakawa iyaye wajen kula da lafiyar ‘ya ‘yansu da karesu daga shiga hatsari.