Wutar Lantarki Mai Karfin Gaske Tayi Sanadiyar Gobara A Garin Minna

A kalla mutane 4 ne suka muku a ciki harda dan Sanda guda da kuma wani mai unguwa, a unguwar Mai Tunbi dake cikin garin Minna fadar gwamnatin jihar Neja, a sakamakon wata gobarar da ta tashi bayan da aka sako hasken wutar lantarki fiye da kima.

Gobarar tayi sanadiyar kona gidaje masu yawa da kuma tafka asara ta Miliyoyin Naira, daya daga cikin mutanen da wannan wuta ta yi wa barna mai suna Mallam Audu Tanko Kaca, yace gidansa ya kone kurmus.

Gwamnan jihar Alhaji Abubakar Sani Bello, ya kai ziyarar jaje ga wadanda wannan lamari ya shafa, haka kuma babban shugaban kamfanin wuta ya yiwa gwamnan bayanin cewa lalle wutar lantarki ce ta haddasa wannan gobara, kuma za a nada kwamitin da zai binciki abinda ya faru.

Ita ma rundunar yan Sandan Nejat ace tana nata bincike kan lamarin inji kakakin yan sandan ASP Bala El-Kana, wanda yace akwai wani insifeta da ya rasu alokacin da yaje ya taimaka, dalilin haka kuma suma suna nan suna bincike.

Kawo yanzu dai al’amura sun lafa a unguwar yayinda a daya gefen ake ci gaba da jaje ga wadanda lamarin ya shafa.

Your browser doesn’t support HTML5

Wutar Lantarki Mai Karfin Gaske Tayi Sanadiyar Gobara A Garin Minna - 2'55"