Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya WHO, ta bayyana cewa mutane a nahiyar Afrika, sun fi lafiya da dadewa a duniya.
Amma hukumar ta ce kimanin miliyoyin mutane ke dauke da manyan cututtuka.
Bayanin ya fito ne a wani taro da hukumar ta gabatar a birnin Dakar na kasar Senegal, inda ta gana da jami’an kiwon lafiya daga kasashe 47 na nahiyar.
Tsawon rayuwa mai inganci a nahiyar ya karu daga shekaru 44.4, zuwa shekaru 53.8, wanda ake kiyasata cewar mutane kan kai wadannan shekaru kamin mutuwa a cewar rahoton na 2015.
Yanzu mutane kan iya kai tsawon shekaru 50.8 zuwa 61.2 cikin koshin lafiya kafin mutuwa.
Matshidiso Moeti, jami’in hukumar da ke kula da nahiyar Afrika, yace wasu dalilai guda biyu suka kawo hakan.
Ku Duba Wannan Ma Jajircewar "Ya'ya Mata Kan Haifar Da Al'umma Mai NagartaNa daya shi ne yadda mutane ke kara samun kulawa musamman masu dauke da cuta mai karya garkuwar jiki HIV-AIDS.
Sannan na biyu, shi ne yadda mutane ke daukan kwararan matakai wajen kariya daga cizon sauro.
Hukumar ta ce na’ukka cututtuka da ke addabar ‘yan Afrika suna sauyawa, haka ma yadda mutuwa ke daukar mutane da suka kamu da ciwo mai karya garkuwar jiki sun ragu, da sauran na’ukkan cututuka da a da suka addabi nahiyar duk sunyi kasa, kamar su cutar cancer, ciwon zuciya, yanzu an rage samun cututtukan.
Amma a bangaren cututtuka da ake kamuwa da su kuwa daga wani mutun zuwa wani tun a shekarar 2000 ba’a sake samun karuwar mace-mace ba.
A bangaren sauran cututukan kuwa sun ragu da kasha 40%.
Ya zuwa yanzu dai hukumomi a nahiyar na jan jiki, wajen daukar matakan gaggawa, da fannin na kiwon lafiya a cewar rahoton.
Haka ma matasa ba sa samun adaddin kulawa da suka kamata su samu, a cewar mai magana da yawun kudurorin Majalisar Dinkin Duniya, Humphrey Karamagi.