Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabuwar Na'ura Mai Saukaka Radadin Ciwo Ga Dan Adam


Idan har bana jin ciwon kai, to zanji ciwon jiki, idan kuwa duk bana jin wadannan to ba shakka zanji ciwon gababuwa da na ciki, a cewar wata mata dake fama da wasu na’ikan cututtuka.

Amma tun daga lokacin da likitana ya bani wani magani da bani bukatar sha ko shafawa, gaskiya yanzu ciwon ya tafi. Likitan yana gudanar da wani bincike wanda yake amfani da wata na’urar da ake kira ‘VR in Hospital and Clinics.’

Ita dai na’urar VR tana daukewa mutum duk wasu zafin ciwo a duk lokacin da mutun yake famada su, domin kuwa takan kawar da hankalin mutum daga duk wani nau’i na radadi da mutum yake ji.

Na’urar dai akan rataya ta a wuya don kallon wasu abubuwa da ke faruwa a wasu duniyoyi, wanda hakan zai taimaka wa mara lafiya wajen kokarin ganin yadda za’a warware matsalolin dake a duniya, ta haka mutum zai manta da radadin ciwon da yake ji a jikin shi.

Marasa lafiya da dama da suka gwada wannan na’urar sun bayyana cewa, lallai ta taimaka musu wajen samun saukin radadin ciwon da suke fama da shi. Hakan na nuni da cewar na’urar zata taimaka wajen ganin mutane sun samu hanyar saukaka zafin ciwon dake damun su a kowane lokaci.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG