WhatsApp Ya Kai Wani Matashi Gidan Kaso

Wani matashi a kasar India ya kwashe watannin biyar a gidan kasa, biyo bayan zargin sa da aka yi a matsayin mai jagorantar wani shafi na matasa a manhajar WhatsApp.

Matashin mai shekaru 21, ya dauki tsawon watanni biyar, bayan wani sako da aka aika a cikin shafin da aka zarge shi da cewar bai cire sakon ba, a matsayin sa na mai kula da shafin “Administrator” a turance.

Iyayen yaron dai sun nuna rashin yardar su da hukuncin da kotun ta dauka, matashin Junaid Khan, dalibi daga karamar hukumar Talen daga jihar Madhya Pradesh ta kasar ta India.

A cewar kamfanin dillancin labarai na “The Times India” jami’an tsaro sun kama matashin tun a watan Fabrairu, a dalilin kasancewar sa mai shugabantar shafin, don haka iyayen sa ke ganin cewar ba’ayi masa adalci ba, idan za’a kama shi da laifin da wani ya aikata don kawai yana mai shugabantar shafin na wucin gadi.

Iyayen matashin sun bayyana cewar dan nasu bai taba shugabantar shafin ba sai a dalilin wasu mambobin shafin sun fita, kuma na’urace ta bashi shugabancin kai tsaye. Don haka su naso a bima dan nasu hakkin sa, da aka rufe shi na watannin shida.