Sabuwar wayar Samsung Galaxy Note 7, wadda kamfanin Samsung ya musanya wa mutane a madadin ta farko wadda kan kama wuta, ita ma ta na fama da wasu matsaloli na batiri, kamar yadda rahotanni ke nunawa, abin da ke janyo fargabar cewa ita ma gyararriyar wayar na da hadari.
Wasu masu wayar, sun ba da rahoton cewa gyararriyar wayar ta Note 7, wadda kamfanin Samsung ya fara bayarwa a makon jiya, bayan da aka janye samfarin farko ta salular a fadin duniya a farkon wannan watan, na da saurin mutuwar batir, ko koda kuwa ana kan caji, haka kuma ance wayar na daukar zabi.
Kamar yadda mujallar Wall Street Journal ta rawaito, kamfanin Samsung ya tabbatar da cewa wasu masu amfani da wayar a Koriya ta Kudu sun koka kan wayar da kamfanin ya musanya saboda ba a iya cire batirin.
Sai dai kuma babu tabbacin ko wayoyi nawa ne wannan matsalar ta shafa, ko kuma mutanen sauran kasashen ma sun fuskanci matsaloli makamantan wannan tattare da wayar da aka musanya din. Kamfanin Samsung dai yace yanzu haka yana gudanar da binciken korafe korafen da aka yi.
Biyo bayan rahotannin dake nuna cewa wayar Note 7 na daukar zafi, wasu lokuta kuma takan yi bindiga, hakan ya tilasta ma Samsung janye Miliyoyin wayar da ya sayarwa al’umma. A wannan mawuyacin lokaci na janye wayoyi kimanin milyan 2 da rabi ganin hukumomi da kungiyoyin kare matafiya kan gargadi masu mayar da su kasha.
Jimlar kudi Dalar Amurka Biliyan 26 ne Samsung ya tafka asara a dalilin wannan janyewar.
Your browser doesn’t support HTML5