Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Google Zai Bayyana Sabuwar Wayar Zamani


ofishin Google
ofishin Google

Kamfanin Google yace zai gudanar da wani buki a wata mai zuwa a birnin San Francisco, inda ake kyautata tsammanin zai fitar da wata sabuwar waya.

An sanar da ranar 4 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za a gudanar da bukin ta wani hotan bidiyo na dandalin Youtube, cikin bidiyon aka nuna akwatin bincike mai kusurwa hudu da siffar waya, sai kuma sauti da yake cewa “zo ka dauki abin da kake so” hotan bidiyon dai bai bayyana sunan sabuwar wayar ba, sai dai ya nuna tambarin google da kowa ya sani G a jikin wayar.

An dade ana jita jitar cewa google zai kirkiri sabuwar waya ta kansa kafin karshen shekara ta 2016, kuma an tsammaci wannan buki da kamfanin zai yi a watan Oktoba wanda zai mayar da hankali wajen sanar da wasu sabbin kirkire kirkire da kamfanin yayi, ciki harda sabuwar waya da manhajar 4K Chromecast ta yanar gizo.

Ana kyautata tsammanin za a kira wayar da suna Pixel da kuma Pixel XL, a cewar wani rahoto da aka fitar farkon watan nan na Android Police, amma babu wani cikakken bayani kan wayar, kamar ranar da zata fito da dai sauransu.

Mai magana da yawun kamfanin google yace, ayi tsammanin wani abin farin ciki da karfe 9 na safe ranar bukin, wanda za a fitar ta yanar gizo kai tsaye, amma yaki ya ci gaba da bayani.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:20 0:00

XS
SM
MD
LG