Hasashen kamfanin zumuntar Facebook, na shekaru biyu akwai kuskure cikin shi. Kamfanin Facebook, yayi hasashen cewar nan da shekaru biyu yawan mutane da suke kallon bidiyo a shafin nasu zai karu da kashi dari bisa dari 100%.
Hukumomin kamfanin sun fitar da wani rahoto da ya nuna cewar, sunyi amfani da wasu lambobi wajen tattara wanna bayanan, amma daga bisani sun iya gane cewar, akwai kuskure a cikin hasashen nasu.
Kamfanin dai sun yi fazukun kimani kashi sittin 60 zuwa tamanin 80 na abun da suka bayyana. Duk dai da ganin cewar yanzu kamfanin, sun samar da wata dama da mutane zasu iya daukar bidiyon kansu, a lokacin da suke gabatar da wani abu da suke son wasu su gani a ko ina a fadin duniya kai tsaye.
Hakan dai wata babbar damace, da mutane zasu dinga aikawa da sako batare da tunanin mutane sai sun karanta rubutu ba, suna iya kallo don kara samun fahimtar mai ake nufi.