Watannin Karshen Shekara: Ku Kai Rahoton Tukin Ganganci Domin Kare Afkuwar Hatsura - FRSC

FRSC

FRSC ta yi wannan kira ne bayan da ta kammala gangaminta na wayar da kan al’umma a kan watannin karshen shekara.

A yau Juma’a, hukumar kare afkuwar hatsura ta Najeriya (FRSC) ta bukaci matafiya su kai rahoton tukin ganganci akan tituna domin rage yawaitar afkuwar hatsura a watannin karshen shekarar bana.

FRSC ta yi wannan kira ne bayan da ta kammala gangaminta na wayar da kan al’umma a kan watannin karshen shekara.

Taken gangamin na bana shine “yi magana a kan tukin ganganci: hatsura sun fi hallaka fasinjoji fiye da direbobi”.

A ranar 6 ga watan Nuwambar da muke ciki, reshen jihar Filato na hukumar ta FRSC ya kaddamar da nasa gangamin wayar da kan al’ummar a birnin Jos.

A jawabinsa yayin bikin kaddamar da gangamin, Kwamandan FRSC na jihar, Maxwell Plateau, ya jaddada bukatar samun sauyin dabi’a a tsakanin direbobi.

Ya jaddada cewa fasinjoji na da hakkin a tukasu cikin aminci tare da karfafa musu gwiwar jan kunnen direbobin da suka karya dokokin tuki.