Gwamnan Kano, Abba Yusuf ya musanta ikirarin samun rashin jitiwa da uban gidansa na siyasa, Sanata Rabiu Kwankwaso, inda yace har yanzu alakarsu mai karfi ce kuma ta ginu ne a kan mutunta juna.
A yayin wata ganawa da manema labarai a Alhamis da ta gabata, Gwamna Yusuf ya yi karin haske game da rade-radin da ake yadawa a tafiyar kwankwasiya dama jam’iyyar NNPP, dake nuna cewa Kwankwaso na yin katsalandan a harkokin gwamnatinsa, inda yake zama tankar “wa’adin mulki na 3 yake yi a boye”.
Gwamna Abba Yusuf ya bayyana kirarin da mara tushe, inda ya jaddada dadewa da kuma karfin dangantakarsa da Kwankwaso.
“Babu kamshin gaskiya game da rade-radin rashin jituwa a tsakaninmu.” a cewar Abba Yusuf. “yau shakarata 40 da saninsa, ku gaya mini, wane dan siyasa ne zai shafe tsawon wannan lokaci ba tare da sun bata ba?”
Ana zargin cewar dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Dala, Aliyu Sani Madakin-Gini, wanda kwanan nan ya raba gari da kwankwason da kitsa jita-jitar.
Madakin-Gini yayi zargin cewar batutuwan da suka shafi kwangilar sayen magunguna data bada gurbin karatu ne suka haddasa tsamin dangantakar. saidai, Abba Yusuf, ya yi watsi da zarge-zargen, inda ya jaddada ikonsa sannan ya yabawa gudunmowar kwankwaso a rayuwarsa ta siyasa.
Dandalin Mu Tattauna