A jamhuriyar Nijar, alkalin wata kotu a birnin Yamai ya karbe wasu yara daga hannun mutanen da ake zargi da safarar jarirai cikinsu har da matar jagoran ‘yan adawa Hama Amadou, domin mayarda su gidan marayu a ci gaba da zartar da hukuncin da mashara’antar kasar ta yanke akan wannan badakala sai dai lauyoyin dake kare wadanan mutane na ganin rashin dacewar wannan mataki.
Yara fiye da goma masu shekaru uku zuwa hudu da haihuwa ne alkali mai kula da shara’ar yara kanana ne ya karbe daga hannun matan dake tsare a kurkuku, a sakamakon hukuncin daya hau kansu bayan da kotun tace ta samesu da laifin safarar jarirai.
A takardan da ya sakawa hannu alkali ya bayana cewa kare mutuncin wadannan yara shine abinda hukuma ke hange, matakin da lauyoyin dake kare wadanda ake tuhuma ke ganin ya sabawa doka. Mallan Ali Kadiri lauyan dake kare matar tsohon kakakin majalisar dokokin Niger, Hamma Amadou, yace hujojin da alkalin ya bada na karbe yaran da kuma aijiye a gidan marayu akwai kuskure a ciki.
Ya kara da cewa a matsayinsu na lauyoyi sunce anyi kuskure domin inda yaran suke suna zuwa makaranta kuma ana basu tarbiyya ta kwarai, abin baiyi ba domin an ci hakkinsu, an hanasu tafiya makaranta. Yana mai cewa baza suyi kasa a gwiwa ba koda zasuje kotun kasa da kasa, ne domin kwato wa yaran hakkinsu.
Shekaru uku aka shafe ana safa da marwa a kotuna domin tantance gaskiyar abinda ake zargin wannan mutane da aikatawa, wanda suka kunshi hamshakan attajirai da wasu fitattun ‘yan siyaysa da matansu. Kafin daga bisani a yanke musu hukuncin zama gidan yari. A tsakiyar watan dake tafe ne wannan mutane dake kiran kansu firsinonin siyaysa zasu kammala zaman kurkukun watanni shida da ya rataya a wuyansu.
Your browser doesn’t support HTML5