A watan da ya shige ne aka kyale daruruwan mata shiga wani filin wasa a birnin Riyadh, inda aka saba gudanar da wasan kwallon kafa, domin halartar wani bukin ranar ‘yancin kai na Sa’udiyya.
JIya lahadi, Hukumar Wasanni ta Kasa ta sanar ta kafofin Social Media cewa “ta fara shirye-shiryen gyara wasu filayen wasanni uku a Riyadh, da Jeddah da Dammam, ta yadda zasu iya karbar iyalai baki dayansu daga farkon shekarar 2018.”
Kasar Sa’udiyya mai akidar ra’ayin rikau, na daya daga cikin kasashen da suka fi takaita walwalar mata a bainar jama’a, kuma ta jima tana da dokokin da suka hana mata shiga filayen wasanni a saboda yadda ba a yarda mata su gauraya wuri guda da maza ba.
Wannan sanarwa ta biyo bayan wata guda a watan da ya shige wadda ta ce daga watan Yuni mai zuwa za a kyale mata su tuka mota.
Har ila yau, ana sa ran Sa’udiyya zata dage haramcin da ta kafa na gidajen sinima, kuma tana karfafa guiwar cudanyar maza da mata a lokacin bukukuwa, abinda ba a taba gani ba a tarihin kasar.
Facebook Forum