Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Ya Nada Boss Mustapha Sabon Sakataren Gwamnati Tarayya


Boss Mustapha Sakataren Gwamnatin Najeriya
Boss Mustapha Sakataren Gwamnatin Najeriya

A yau Litinin ne shugaba Muhammdu Buhari ya bada sanarwar nada Boss Mustapha, a matsayin sabon sakatren gwamnatin tarayya ta hanun kakakin fadar shugaban kasa Femi Adesina.

Kafin shugaba Muhammdu Buhari ya nada Boss Mustapha a matsayin sabon sakataren gwamnatin tarayya, Boss, shine Darekta Janar na hukumar kula da hanyoyin ruwa na cikin kasa.

Mustapha, zai maye gurbin Babachir David Lawal, wanda aka dakatar sakamakon zargin cuwa-cuwa da kudaden tallafawa ‘yan gudun hijira. Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da Babachir Lawal tare da Darekta Janar na hukumar leken asiri ta Najeriya NIA, Mabasada Ayo Oke.

Binciken da kwamitin majalisar dattijan Najeriya karkashin jagorancin sanata Shehu Sani, ya gano karkata wasu kudade sama da milyan 270 da sunan yanke wasu ciyayi da suke hana walwala a cikin ruwa a jahar Yobe.

Darekta Ayo Oke, an dakatar da shi ne bayan da hukumar EFCC ta gano kudi Dala milyan 43 da yace mallakar hukumar ne a wani gida a Legas.

Babu Karin bayani daga cikin sanarwar ko tsofin jami’an biyu zasu fuskanci shari’a kan wannan batu.

Domin karin bayani, saurari rahoton Umar Faruk Musa daga Abuja.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00
Shiga Kai Tsaye

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG