Wata Makaranta a Kano Za Ta Fara Karban Kudin Yanar Gizo a Matsayin Kudin Makaranta

SCIENCE ACADEMY KANO

Wata makaranta mai zaman kanta mai suna New Oxford Science Academy dake jihar Kano ta ce ta amince da fara karbar kudin yanar gizo crypto currency a matsayin hanyar biyan kudin makranta.

Shugaban wannan makaranta ya ce kasashen da suka cigaba tuni suka dade suna amfani da kudin yanar gizo ko kuma crypto-currency a turance a matsayin wata hanyar karbar kudin da za’a yi musayar cinikayar da su .

Bisa ga cewar shi, wannan ne ya sa suka amince da fara amfani da sabon wannan tsari na karbar kudin makaranta ta hanyar yanar gizo domin sajewa da sauran kasashen da suka cigaba a duniya.

A hirar shi da Muryar Amurka, Sabiu Musa Haruna, shugaban makarantar New Oxford Science Academy dake Kano, ya kuma ce sun shigo da tsarin ne kafin lokaci ya kure musu gannin da yadda ake amfani da wannan hanya a wasu kasashen.

Ya ce gwamnatin Najeriya bata hana wannan tsari ba kamar yadda wasu suke tsammani. Kuma a yanzu haka iyayen yara goma sha biyar ne suka biya kudaden makarantar yaransu ta hanyar crypto currency.

Daya daga cikin iyayen da suke amfani da wannan tsari a wannan makaranta, Muftahu Sani Baban Yara, ya ce yana biya wa yaransu biyu kudaden makaranta ta hanyar amfani da crypto currency bayan da guda daya da yake daukar nauyinsa a jami’a.

Wani masanin harkar kasuwanci da ke jami'an Federal University Dutse, Dr Abbdulnasir Turawa ya ce ba halartaciyyar hanya ce ba wata makaranta ko biyan kudaden kasuwanci ta crypto currency.

Duk da cewa wasu kasashe sun amince da wannan tsari amma mafi yawan wadannan kasashen suna da dokokin da suke tare da hakan wanda Najeriya bata da wannan doka, dalili ke nan da sa ya zama haramtattaciyar hanya kuma ya saba wa tsarin doka.

Ya ce har kawo yanzu babban banki bai halarta amfani da wannan kudi na crypto ba wajen gudanar da cinikkaya kuma har yanzu babu wata doka da ta amince da hakan.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Wata Makaranta a Kano Za Ta Fara Karban Kudin Yanar Gizo a Matsayin Kudin Makaranta