'Yan Najeriyan sun bayyana cewa, wani lokaci ya kan dauki makonnin ko kwanaki kafin kudin da ‘yan ciranin da ke Amurka suke turawa kafin ya kai ga danginsu a Najeriya.
Ben Eluan da Osezele Orukpe, injiniyoyin biyu da suke zaune a Najeriya, sun fuskanci wannan matsala a cikin shekarar 2019. Sun yi wa wani abokin huldar kasuwancin su da ke a Burtaniya aiki, kuma da lokacin da ya kamata a biya su kudin aikin su ya yi, an biya su ne da manhajar Skrill. Duk da haka, an dauki mako daya kafin su samu kudin, kuma sun yi asarar kudi da yawa daga cajin da aka yi musu.
A cikin hira da wani dandalin ayyukan fasaha da ake kira TechCrunch, Eluan ya bayyana cewa, “Wannan ya sa mun yi tunanin kudin da aka biya, da kuma mafi muhimmanci, biyan kudaden zuwa kasashen ketare,” “hanyar samun kudi ta leburanci da kuma na kananan masana’antu na da matukar girma, kuma muna da sha'awar bunkasar su sosai don haka mu ka sadaukar da lokacinmu gaba daya wajen samar da hanyar biyan kudade zuwa Afirka."
A cikin shekaru uku da suka gabata, kamfanoni tura kudaden yanar gizo na zamani da ake kira crypto da kuma tsarin gudanar da harkokin kasuwanci da ba shi da goyon baya ko sa hannun gwamnati da ake kira fiat, suna cike wannan gibin.
Matakin da Elun wanda shi ne jami'in zartaswa na kamfanin, da kuma abokinsa Orukpe babban jami'in gudanarwa da binciken kamfanin suka dauka wajen kirkiro da kamfanin Flux. An gina kamfanin tura kudin crypto ne don bai wa 'yan kasuwa dama su tura ko su karbi kudin daga ko ina a duniya.