KANO, NIGERIA - Hukumar lafiya ta duniya da kwararru a fagen cimaka sun ce galibin cutukan dake barazana ga rayuwar bil’adama a yanzu suna da alaka da yanayin nau’in cimakar mutane.
Sai dai baya ga talauci da fatara, karancin aiki da masana kimiyyar abinci a wasu daga cikin asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya a galibin kasashen Afirka irin su Najeriya na zama babban kalubalen kiwon lafyar jama’a a nahiyar.
Dietician Zaitun Aminu Mahmud na cibiyar nazarin kula da harkokin lafiyar cimaka ta Najeriya na cewa, “Tunda abinci ya zama dole a ci, to haka cututtukan idan muna so mu sami saukinsu tilas mu tantance me ya kamata mu ci, mene bai kamata mu ci ba. Mutane har yanzu ba su waye da muhimmancin wannan fanni ba, haka suma hukumomi da gwamnatocin mu ba sa baiwa wannan bangare kulawar data kamata, kamar yadda ake yi a sauran bagarori na duniya.”
To sai dai domin magance wannan kalubale ne, kungiyar WANDA Organization ta dauki nauyin karatun wasu dalibai mata su 25 dake karatu a wannan fanni a jami’ar Bayero Kano kuma har ma ta shirya musu bitar kara ilimi a Lahadin da ta gabata.
Dr. Ashiru Abubakar wanda ya jagoran shirya bitar ya ce daliban sun fito ne daga iyalai masu rangwamen karfin tattalin arziki.”Abin da muka yi shine yadda zamu tallafi yara mata wadanda suke karantar darrusan cimaka da harkokin noma a nan Najeriya ta hanyar biya musu kudin makaranata”.
Daliban da suka ci gajiyar wannan tsari na kungiyar ta WANDA Organization sun bayyana godiya tare da alkawarin jajircewa akan harkokin karantunsu domin samun nasara.
Duk da tallafi daga kungiyoyi irin su kungiyar WANDA Organization da dedekun mutane dama wasu daga cikin gwamnatoci, dalibai da yawa dake karatu a jami’o’in Najeriya sun hakura da karatu biyo bayan mummunan karin kudin makaranta a jami’o’in kasar a shekarar karatu ta bana.
Saurari cikakken rahoto daga Mahmud Ibrahim Kwari:
Your browser doesn’t support HTML5