Sashin sa ido kan baranar kutse na Kamfanin manhajar, ya ce har yanzu kungiyar na ta kokarin yin kutse ga mutanen da ke da alaka da Biden, Trump, da kuma Mataimakiyar Shugaban Kasa Kamala Harris, wadda ta maye gurbin Biden a watan jiya, a matsayin ‘yar takarar Shugaban kasar ta jam’iyyar Democrat, bayan da ya janye.
Google ya ce wadanda aka auna a yinkurin kutsen, sun hada da jami’an gwamnati na yanzu da na da, da kuma jami’an yakin neman zabe.
Wannan sabon bayanin da ya fito daga sashin nazarin barazanar kutse na kamfanin na Goodle, ya tabbatar da rahoton kamfanin manhajar Microsoft na ranar Jumma’a, wanda ya bayyana cewa, akwai wani yunkurin kutse ga harkokin zaben Shugaban kasar Amurka na wannan shekarar, daga wata kungiyar kutse ta kasar Iran.
Rahoton ya ce Google ya lura da yadda kungiyar ta iya kutse a akwatin sakonnin Gmal na wani babban mai ba da shawara kan harkokin siyasa. Google ya kai rahoto ga hukumar FBI a watan Yuli. Rahoton na Microsoft na ranar Juma'a ya yi fitar da bayanai iri daya, ya kuma ce, an yi kutse a imel na wani tsohon babban mai ba da shawara ga yakin neman zaben shugaban kasa aka aika sakon badda sawu ga wani babban jami'in kamfen.
Kungiyar ta saba da hanyar sa ido na Google da sauran masu bincike, kuma wannan ba shi ne karon farko da ta yi kokarin shishigi a zaben Amurka ba, in ji Hultquist. Rahoton ya kara da cewa kungiyar Iran din ta nemi yin kutse a yakin neman zaben Biden da Trump a shekarar 2020, a watan Yuni na wannan shekarar.
Rahoton ya ce kungiyar ta kuma yi fice a sauran ayyukan leken asiri ta yanar gizo, musamman a yankin Gabas ta Tsakiya. A cikin 'yan watannin nan, yayin da yakin Isra'ila da Hamas ke kara ta'azzara da tada hankali a yankin. Wannan aiki ya hada da kokarin yin kutse a imel na jami'an diflomasiyya na Isra'ila, da malaman jami'o'i, kungiyoyi masu zaman kansu da kuma sojojin da ke da alaka da su.
Ofishin yakin neman zaben Trump ya fada ranar asabar cewa, an yi masa kutse kuma an sace wasu muhimman takardu tare da rarraba su. Ya bayyana cewa Iraniya ne ke da alhakin kutsen.
Haka kuma jaridar Politico ta bayyana cewa, ta sami wasu bayanan yakin neman zaben Trump da aka tura ta hanyar imel da aka kwarmata. ko da yake ba a bayyana ko takardun da aka fallasa na da alaka da ayyukan intanet na Iran da ake zargi ba. Jaridar Washington Post da New York Times su ma sun sami takardun.