Wata Kungiya Ta Ce Magance Matsalolin Najeriya Na Bukatar A Hada Kai Da ‘Yan Jarida

Wata kungiya mai fafutukar samar da gwamnatoci na gari da kuma adalci wato Network For Good Governance and Justice ta ce idan har ana so a magance matsalolin Najeriya dole a hada kai da 'yan-jarida.

KADUNA, NIGERIA - Kungiyar wadda ta shirya taron bita kan kalubalen da ke bangaren shari'a wajen samar da gwamnati ta gari da kuma bukatar inganta aikin jarida don kyautata damakadiyya ta ce aikin jarida jigo ne a dukkan lamurran ci gaban kasa.

Farfesa Sadiq Isah Radda wanda shine shugaban kwamitin amintattu na kungiyar ta Network For Good Governance and Justice ya ce duk da yawan matsalolin Najeriya akwai mafita.

Farfesa Isma'il Shehu na Jami'ar Amadu Bello dake Zariya shine ya gabatar da mukala kan inganta aikin jarida do kawo ci gaban kasa.

'Yan-jarida da dama ne dai su ka halarci wannan taron bita kuma sun ce sun fa'idantu.

A farkon shekara mai zuwa ne dai za a gudanar da zabubbuka a fadin Najeriya, kuma tuni kungiyoyi su ka dukufa wajen shirya tarurrukan wayar da kan al'ummar kasa game da zaben shugabanni na gari.

Saurari rahoto cikin sauti daga Isah Lawal Ikara:

Your browser doesn’t support HTML5

Wata Kungiya Ta Ce Magance Matsalolin Najeriya Na Bukatar Hadin Kai Da ‘Yan Jarida