Wata Hukumar Bincike a Nigeria tace ta gano cewa lalle sojan kasar sun hallaka ‘yan Shi’a 348, don haka tana son a gurfanar da masu hannu cikin kisan a gaban shara’a don hukunta su.
WASHINGTON DC —
Hukumar binciken ta fada a cikin rahotonta da aka wallafa jiya Litinin cewa sojan Nigeria sun hallaka wadanan mutanen ne a cikin samamen kwannaki ukku da suka kai akan birnin Zaria, wanda tace kan haka ne take son a bankado ainihin sojojin da suka yi kisan, don ayi musu shara’a.
A cikin watan Disambar shekarar da ta gabata ne dai wannan al’amarin ya afru a can birnin na zazzau, lokacinda sojan suka abkawa hedkwatar madugun ‘yan Shi’ar, Sheikh Ibraheem Zakzaky. Akwai wani soja daya da shima ya rasa ransa, kuma shima Sheikh Zakzaky din an ji mishi rauni. Rundunar sojan Nigeria dai ta bada hujjar kai harin a bisa dalilin cewa ‘yan Shi’ar sun nemi su kashe babban kwamandan sojojin Nigeria ne.