Shugaban kungiyar Farfesa Abdullahi Danladi, shine yayi magana a wani taron manema labarai. Inda yace suna kira ga kakkausar murya ga gwamnatin Najeriya da jami’an tsaron da ke rike da Mallam da iyalinsa, tun bayan abin da ya faru a Zariya. A cewar Danladi sun sami labarin cewa Mallam na fama da ciwon ido mai tsanani, kuma likitan da ke kula da shi yace an kure iliminsa.
Haka nan a karon farko ita dai wannan kungiya ta yi magana kan rahotan kwamitin da gwamnatin jihar Kaduna ta kafa ya mika, game da hatsaniyar da ta faru tsakanin mabiya masahabar Shi’a da rundunar soja a birnin Zariya.
Duk da yake kwamitin yace rahotan na sirri ne ba zasu fadi abin da ke cikin rahotan ba, dole ne a fara mika shi ga gwamnatin domin ta duba shi kafin ta sanar da al’umma abin da ya kunsa.
Saurari cikakken rahotan Isah Lawal Ikara da jihar Kaduna.