Gwamnatin dai tace ko bayan bayyana sakamakon wannan rahoto da tayi a daren ranar Lahadi, yanzu haka tana jiran sabon kwamiti na musamman da ta kafa wanda aka bashi makonni biyu domin ya yi nazarin rahotan da kwamitin binciken ya kawo ya kuma baiwa gwamnati jihar Kaduna shawara cikin makwanni biyu.
Mai magana da yawun gwamnan jihar Kaduna, Mr Samuel Aruwa, yace kamar yadda mai girma gwamna yayi alkawari zai bayyana rahotan domin kasa baki daya su karanta su ga abin da aka samo, a jiya gwamnatin ta bayyana rahotan domin sauke nauyin da ta dauka.
Duk da yake rahotan ya nuna cewa kowanne bangare na da laifi, amma mabiya mazhabar Shi’a sunce suna da tantama da tababa game da rahotan mai ‘dauke da shafi 193.
Saurari cikakken rahotan Isah Lawal daga Kaduna.