Wasu masu ababen hawa sun koka akan yadda suke shan wahala kowacce shekara musamman a lokacin bukukuwan Kirsimeti saboda matsalar mai, amma da lokacin ya wuce sa man ya wadatu.
A yayinda na gwamnati ke saidawa, akwai wasu gidajen man dake wuce makadi da rawa. Alhaji Usaini Abbkar, direban mota ne wanda ya bayyana cewa gidajen mai dayawa suna da man amma basa so su saida. Ya kuma ce su kan boye sai da dare su saidawa ‘yan bumburutu.
Lokuta dayawa akan zargi dillalan man fetur masu zaman kansu na IPMAN da masu dakon mai akan cewa su ke boye man a wannan lokacin domin cin kazamar riba. Amma shugabannin kungiyoyin biyu sun sha musanta wannan zargin.
Alhaji Abdulmalik Bello, mataimakin shugaban NATO a shiyar Yola wanda kuma kusa ne a kungiyar IPMAN, yace rashin sani ne ke sa ake yi masu wannan zargin. Babban dalilin matsalar man a yanzu shine babu isasshen man a kasa saboda matatan man Najeriya ba asa iya sarrafa man da zai ishi ‘yan Najeriya.
Ga karin bayani cikin sauti daga Ibrahim Abdul'aziz.
Your browser doesn’t support HTML5