Har yanzu ana fuskantar dogayen layuka a gidajen man fetur a biranen Lagos da Abuja da ma wasu sauran jihohi a Najeriya.
Kamfanin man Fetur na Najeriya, NNPC ya ce man da zai samar wa kasar ya kai kimanin lita miliyan dari bakwai da hamsin da za'a yi anfani dashi cikin kwanaki 21. Ke nan a duk rana ta Allah za'a samar wa Legas tankunan man Fetur dari uku.
Amma a cewar wasu 'yan kasuwa mazauna birnin Legas, suna ganin lamarin tamkar gazawar gwamnatin Najeriya ne duk da alkawarin da ta yi na samar da man a kasa ba tare da shigo dashi daga kasashen waje ba.
A cewar Alhaji Danladi Auyo, Shugaba Buhari har yanzu yana kallon Najeriya da idanun lokacin da ya yiwa kasar mulkin soja ne. Shugaban ya manta yanzu ba lokacin da ba ne. Ya dauki alkawarin daina shigo da mai domin wai, zai tabbatar matatun man kasar suna aiki dari bisa dari. Hakan bai samu ba inji Alhaji Auyo saboda shugaban bai san Najeriyar yau ba.
Akan dogayen layukan da ake fuskanta, 'yan Najeriya masu hada-hadar yau da kullum sun bayyana ra'ayoyinsu. Malam Huseini, wani mai sana'ar acaba ya ce wasu gidajen man sun bude amma cike suke da jama'a, idan kuma har mutum ya samu to sai ya kara kudi na daban daga wanda masu sayar wa zasu jefa aljihunsu. Inji Huseini ko mutum bai kara kudi ba masu sayar da man suna rage adadin abun da suke ba mutane. Ya roki gwamnati ta tabbatar da man ya wadatu.
Wani ya ce akwai mai, amma yawancinsu ba sa son sayar wa domin suna son cin kazamar riba. Amma ya ce an fara samun man, lamarin da ya ce watakila masu sayar da man sun fara jin tsoron Allah ne.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.
Facebook Forum