Wasu 'Yan Mata 4 Sun Kirkiro Sabuwar Manhaja

Wadansu matasa ‘yan mata hudu ‘yan makarantar sakandire na shirin isa birnin California, na kasar Amurka, don gabatar da wata manhaja da suka kirkira da niyyar sayar da ita ga manyan kamfanoni. ‘Yan matan sun kirkiri manhajar da zata taimaka wajen magance matsalar gobara a wayoyin hannu.

'Yan matan dai su hudu wadanda suka lashe gasar matasa masu hazaka ta duniya da aka gudanar a kwankin baya, inda suka doke sauran matasa 19,000 da suka shiga gasar, wadannan 'yan mata sun fito ne daga kasar Palestine.

Haka kuma wadannan ‘yan mata, dalibai ne a makarantar sakandire a matakin aji SS2, wadanda iyayensu suka fito daga kasashen larabawa, kuma iyayensu ba masu hali bane, sun fito daga yankin da ake fama da matsalolin da suka shafi tsaro, biyo bayan rikece rikecen Falasdinawa da Isra’ila.

Yankin dai na fama da matalolin kabilanci musamman na ilimin ‘ya'ya mata, wanda ake daukarsa a matsayin abu da ya sabama al’ada, ‘yan matan sun bayyana jin dadin su, kasancewar zasu yi tafiya a jirgin sama a karon farko a tarihin rayuwar su.

Suna murna da wannan nasarar wadda suke sa ran haduwa da wasu mutane daga ko ina a fadin duniya, a cewar daya daga cikin ‘yan matan Wasan al-Sayed mai shekaru 17, “Muna cike da farinciki, domin kuwa zamu je birnin da ya shahara a duniyar kimiyya da fasaha Silicon Valley, wanda muke sa ran haduwa da mutane daga ko ina a duniya masu hazaka.”