Saudat Suleman Musa, ta ce ta zabi sayar da takalman maza domin a cewarta maza sun fi biyan kudi akan kari sakamakon basa wasa da bashi sabanin yadda cinikaiya take tsakinan mata.
Ta kara da cewa idan namiji ya sayi kaya ko domin ya kare gimansa zai biya akan lokaci duk kuwa da cewar mata sun fi yawan sayen kaya, dan haka Malama Saudat ta bayyana cewa a irin nata tsarin, ta fi son kulla cinikaiya da magidanta.
Matashiyar ta kara da cewa ta fara sana’a ne tun tana aji uku a jami’a domin kau da yawaitar tambayar iyaye kudin kashewa, kuma ko da ta fara taba baiwa shaguna ne a kan sare domin su sayar mata tana kuma bin karamar riba
A cewar ta babban abinda ya sa ta dunguma ga sana'a shine, domin kadabayan ta kammala karatu ta rasa kudaden kashewa a hannun ta.
Daga karshe ta ja hankalin 'yan uwanta mata da su jajirce wajen neman sana’a maimakon su dora nauyinsu ga iyaye ko saurayi, idan mace bata yi aure ba ta iya tsayawa a kan kafafun ta, martabar diya mace sana'a don kare mutuncinta.
Facebook Forum