Kowanne rai yana kaunar mai dadada masa, kuma kamar yadda masu iya magana kan ce, kyauta bata kadan kuma. daya daga cikin alamun so sun hada da kyauta, koda wacce iri ce.
Tarihi ya nuna cewa tun asali masoya kan ba abokan soyayyarsu kyauta sai dai hanyar da ake bayar da kyautar ta banbanta da yadda matasa kan yi a wannan zamanin da muke ciki.
Kamar yadda Malam Murtala Yako, ya bayyana mana a lokacin da muke zantawa da shi ta wayar Tarho, shekaru hamsin da suka gabata, matashi bashi da hurumin daukar kudi ya mikawa budurwa a lokacin zance, domin a al'adance kamata yayi ya bada duk wata kyauta ta hannun magabatan sa.
Kamar yadda muka saba a kowanne karshen mako, shirin samartaka na Dandalinvoa kan nemi jin ra'ayoyin matasa maza da mata akan batutuwa daban daban da suka shafi harkokin yau da kullum, soyayya, zamantakewa da makamantan su.
A wannan karon mun nemi jin ta bakin matasa ne akan tambaya kamar haka, shin kyautar da saurayi zai ba budurwa wurin zance na da kima ko adadi?. ana iya biyo mu a shafin mu mai adireshi www.dandalinvoa.com ko kuma shafin mu na voahausafacebook, domin a bayyana ra'ayi.
Facebook Forum