Wasu da ba a tantance ko su wanene ba, sun harbe shanun makiyaya a yankin Kwall, dake karamar hukumar Bassa a jihar Filato, da yammacin ranar Alhamis.
WASHINGTON DC - —
Wannan lamari ya auku ne bayan wani zama na musamman don sasantawa tsakanin al’ummomin yankin don samun dawwamammen zaman lafiya.
Ardon karamar hukumar Bassa, Alhaji Umar Dakare wanda ya shaidawa Muryar Amurka cewa an kashe shanu kusan dari, aka kuma tafi da wadansu, ya yi kiran jama’ar yankin su bar hukumomi su gudanar da bincike.
Shima shugaban matasan kabilar Irigwe, Shinge Dodo Justice, ya ce wasu marasa son zaman lafiya ne ke neman maida musu hannun agogo baya kan zaman lafiyar da suka samu.
Ardon Riyom, Alhaji Mato Ibrahim wanda ya ce shanun mutanensa ne aka kashen, ya jaddada bukatar hukuma ta biyasu diyya don a zauna lafiya.
Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5