Hukumar Shippers Concil ta kai ziyara ta musamman ga rundunar sojojin ruwa domin kulla yarjejeniya da samar da kyakkyawar alaka domin hada karfi da karfe domin cimma manufar.
Shugaban hukumar Hassan Bello, ya ce wannan ziyara ta na da matukar muhimmanci ganin yadda jiragen ruwa ke hada-hada wadanda tabbas suna bukatar tsaro, biyo bayan irin fashi da makamin dake faruwa cikin ‘yan shekarun nan.
Haka kuma shugaban ya yaba da kokarin da rundunar sojojin ruwa suke yi na tabbatar da cewa duk jiragen ruwan da zasu shiga Najeriya an basu matakan tsaron da suke bukata.
Rashin daukar matakan tsaro ga kayayyakin da ake shiga Najeriya da su ta ruwa, kan haifar da matsaloli masu yawa ciki har da tashin farashin kayayyakin wanda hakan kan iya shafar tattalin arzikin kasar.
Shima babban hafsan sojojin ruwa vice admiral Ibok Ekwe Ibas, ya ce ziyarar abu ne mai kyau, kuma hakkin rundunar ce ta samar da tsaro a iyakokin kasar domin habaka tattaln arziki da kuma ci gaban kasa.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Hauwa Umar.
Facebook Forum