A yau ne Rundunar sojojin Ruwan Amurka da ke Afirka wato U.S., NAVAF, ke jagorantar atisayen sojojin ruwa na kasashen duniya a Najeriya, atisayen da dakarun ruwa na fiye da kasashe 30 ke taka rawa a ciki.
Kakakin hedkwatar Rundunar sojojin Ruwan Najeriya, Navy Commodore Suleiman Dahun ya bayyana cewa manyan jiragen ruwan yakin Najeriya irin su NNS Centenaru da NNS Unity tare da sauran jiragen yakin kasashe mahalarta ne za su yi atisayen.
Commodore Dahun ya ce, tuni jiragen ruwan yakin Amurka, Morocco Portugal da ma na karin wasu kasashen Afirka 20 duk sun iso Najeriya don taka rawa a wannan atisaye na "Obangame Express."
Tun da farko sai da kwamandan sojojin ruwan Amurka da ke Afirka, Admiral James Faggo, ya bayyana cewa makasudin wannan atisaye shi ne don samar da tsaro a gabar tekun Guinea,
Wannan dai shi ne atisayen jiragen yakin sojojin ruwa mafi girma a duniya wanda Amurka ke shiryawa, da za a shafe shekaru biyar ana yi a Najeriya da rundunar sojin ruwan kasar ke karbar bakuncinsa.
Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina daga Abuja: