‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 14 A Jihar Filato

Yan bindiga

Mutane 14 ne 'yan bindiga suka hallaka a kauyen Ari Doh, da aka fi sani da Gidan Ado, da ke yankin Ganawuri a karamar hukumar Riyom da ke jihar Filato a Najeriya, yayin da wasu mutane uku da suka sami raunuka ke kwance a asibiti.

A daren Lahadi ne wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su wanene ba, suka mamaye garin da galibin mazauna cikinsa ‘yan kabilar Irigwe ne daga Bassa hari da tsakar dare, tare da hallaka mutane 15 tare da jikkata mutane da dama a harin.

Kakakin kungiyar matasan kabilar Irigwe, Joseph Chudu ya shaida cewa 'yan bindigar sun hallaka mutane 14.

A gefe guda kuwa, Rabaran Andrew Moria na majami'ar COCIN RCC Ganawuri ya ce sun binne mutane goma sha biyar, ciki har da mata uku dauke da juna biyu da ke dap da haihuwa.

Hakazalika, sanarwar da shugabancin kungiyar ci gaban kabilar Irigwe ya rabawa manema labarai a garin Jos, dauke da sa hannun sakataren yada labaranta na kasa, Sam Jugo ta ce maharan sun hallaka mutane 15.

Da yake bayyana damuwa game da harin da aka kai ba tare da wani dalili ba sa’o’i kalilan gabanin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara, shugabancin kungiyar ya bukaci hukumomin tsaro, su tabbatar da hana afkuwar irin wadannan munanan al’amura a nan gaba tare da yin jan kunne a kan hare-haren ramuwar gayya.

Kokarin jin martani kan zargi da ake yi wa sojoji da hannu a kisan, ya ci tura, duk da sako da wakiliyar Muryar Amurka ta aike wa kakakin rundunar Operation Safe Haven da ke wanzar da zaman lafiya a jihar Filato, Manjo Samson Nantip Zhakom ta kafar WhatsApp, bai maido da amsa ba.

Haka ma hukumomin jihar da na karamar hukumar Riyom ba su ce komai kan kosan ba, har lokacin hada wannan rahoto.

Tun farko dai, rundunar 'yan sandan jihar Filato ta ce ta baza jami'anta a kananan hukumomi goma sha bakwai na jihar don tabbatar da tsaro a lokacin bukukuwan Kirsimeti.

Rundunar 'yan sandan ta hana kiwon dabbobi da yin noma da dare, ta kuma sanya dokar takaita lokacin bude gidajen barasa, da dakatar da tonon ma'adinai da dare, da takaita ayyukan babur a kananan hukumomin Bassa, Barkin Ladi, Riyom, Bokkos da Mangu.

Ko a ranar 24 ga watan Disamban bara ma, 'yan bindiga sun hallaka daruruwan mutane, akasarinsu a kananan hukumomin Mangu da Bokkos a jihar ta Filato.

Saurari cikakken rahoto daga Zainab Babaji:

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutm 14 A Kauyen Ari Doh, Jihar Filato.mp3