Wannan na zuwa ne lokacin da jami'an tsaro ke ta kama ‘yan bindiga duk da cewa ayyukkan ta'addanci na ci gaba da wanzuwa.
Duk da yaki da ta'addanci da ake yi a Najeriya har yanzu bai kawo karshen ayyukan na ta'addanci ba, wasu lokuta jami'an tsaro kan samu galaba akan ‘yan ta'addar ko su kashe, ko su kama su da rai.
Ko a wannan makon ma rundunar 'yan sandan Najeriya ta kama mutane tara da take tuhuma da aikata ta'addanci a sassa daban daban na Sakkwato dake arewa maso yammacin kasar, wadanda kwamishinan 'yan Sandan Muhammad Usaini Gumel ya ce sun hada da daya daga cikin barayin daji da suka sace wani mutum dan shekara hamsin da biyar, suka boye shi, suka nemi a biya kudin fansa. Bayan an kai musu kudin fansar maimakon su saki dattijon, sai suka hallaka shi.
Yace daya daga cikin wadanda suka kai kudin fansar ne ya gane daya daga cikin barayin lokacin da ya je asibiti neman magani, nan take ya sanar da ‘yan sanda suka kame barawon kuma da aka bincike sa ya amsa laifin sa kuma ya tabbatar da cewa yana tare da gungun ‘yan ta'adda da suka yi wannan aika-aikar.
Wani abin dake daukar hankali shi ne yadda wadanda ake kamawa ke fadawa duniya ta'addancin da suka aikata duk da yake suna hannun hukuma, kamar wani da aka kama da yace sunan sa Aminu. Ya ce sun je gidan wani mutum suka buge shi sai suka yi masa satar kudi har aka kama su. Ya kara da cewa kaddara ce ta sa su yin haka.
Shi kuma wani mai suna Arinze yace shi dan kasuwa ne, gobarar da ta kone kasuwar Sakkwato tayi sanadin shigar sa mawuyacin hali, daga nan ya soma tunanin shiga muguwar safara ta ta'addanci domin ya samu kudi.
Masana lamurran tsaro na ganin cewa akan wannan batun akwai abubuwa da ya kamata a duba wadanda ke nuna ko mahukunta da gaske suke fada da ta'addanci ko akasin haka.
A hirar shi da Muryar Amurka, Dokta Yahuza Getso wanda kwanannan ya tsalleki rijiya da baya daga hannun ‘yan bindiga na ganin cewa, da gwamnati na yin abinda ya dace, da yanzu an kawo karshen matsalar rashin tsaro.
Yace ai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bada umurnin a harbe duk wanda aka kama rike da bindiga AK 47 wanda bai cancanta ya rika ta ba, amma ga su nan ana ta kamawa ana yi musu tambayoyi ba wanda aka taba jin an harbe.
Hakan ya nuna an kasa bin umurnin shugaban kasa kuma hakan na iya nuna cewa ba da gaske ake fada da ta'addanci ba.
An jima ana kama wadanda ake tuhuma da aikata ayyukan ta'addanci da suka kunshi rukunnan al'umma daban-daban ciki har da su kansu jami'an na tsaron, amma yana da wuya aji hukuncin da ya biyo baya. Abinda masanan ke gani ya zaman babbar illa ga yaki da ta'addanci.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5