Rundunar ‘yan Sandan jihar Neja ta cafke wasu ‘yan banga biyu da ake zargin suna da hanu wajan hadasa rikicin da yayi sanadiyar hallaka mutane tare da hasarar dukiya a garin Kontagora.
Da Yammacin Alhamis din data gabata ne dai wasu matasa a Komtagora suka fusata suka kona ofishin ‘yan bangan saboda kisan gillar da suka ce ‘yan bangan sun yiwa wani matashi, alamarin da ya jawo zaman dar dar a garin na Kontagora.
Kakakin ‘yan Sandan jihar Neja, DSP Bala Elkana, y ace rundunar na ci gaba da bincike kuma zasu tabbatar an hukunta duk masu hannu a tashin hankalin da ya afku a garin Kontagora.
Da muryar Amurka ta tuntubi shugaban kungiyar ‘yan banga na jihar ta Neja, mataimakin Sufeto janar na ‘yan Sanda mai ritaya Ibrahim Machi, y ace bashi da cikakken bayani kawo yanzu.
A halin da ake ciki Gwamnatin jihar Neja, ta nuna rashin jindadinta akan wannan alamari a saboda haka ma take kiran jama’a da a kai zuciya nesa.
Your browser doesn’t support HTML5