Kusan sa'o'i 48 da hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta ke ci gaba da kai samame a kan kasuwar 'yan canjin bayan fagge dake unguwar zone 4 na birnin tarayya Abuja, masana tattalin arziki sun ce wannan ba shi ne mafita ba kuma ba 'yan canjin kasuwannin bayan fagge ke yi wa tattalin arzikin Najeriya gagarumar illa ba, wasu shuwagabannin bankunan kasuwancin kasar ne.
Masana tattalin arzikin dai sun jadada hakan ne a daidai lokacin da farashin dala a kan Naira ya kai sama da dubu 1 da 800 a yau Laraba, 21 ga watan Fabrairu.
A nasa bangare masanin tattalin arziki, Mallam Kasim Garba Kurfi ya ce kamata ya yi gwamnati ta binciki bankunan kasuwancin kasar don su ne ke cin riba da lamarin idan dai ana son a warware bakin zaren matsalar karanci da tashin farashin dala a kasuwanni.
Shi ma Shugaban Kungiyar ‘Yan Canjin Kasuwannin Bayan Fagge, Alhaji Aminu Gwadabe ya ce yanayin tashin farashin dala baya rasa nasaba da batun karanci da neman da ya fi karfin bukatu baya ga wasu ‘yan Najeriya mazauna waje dake sana’ar yada jita-jitan farashi, sai kuma wasu kafaffen yanar gizo da ke kayyade farashi ba bisa ka’ida ba.
Tun ba yau ba ake zargin bankunan kasuwancin Najeriya da abun da ake kira ''round tripping'' a turance wato boye kudadden kasar waje kamar dala don sayarwa ta kofoffin da ake samun kazamar riba, lamarin da muka tuntubi babban bankin kasar don jin matakin da zasu dauka kan wannan zargi amma duk kokarin ya ci tura bayan kira ta wayar tarho da barin sakon ko ta kwana ga Sashen Sanya Ido a kan Bankunan Kasuwancin wato Department of Banking Supervision.
Alkaluman shekara-shekara da ga shafin FMDQ sun yi nuni da cewa a karshen shekarar 2023, darajar Naira ta fadi da kaso 96.55 cikin dari a kan Naira 907.11 a kowacce dala idan aka kwatanta da Naira 461.61 da aka samu a karshen shekarar 2022 a kasuwar musayar kudaden waje ta Najeriya wato NAFEM.
A saurari cikakken rahoton Halima Abdulrauf:
Your browser doesn’t support HTML5