Wasu Matasa Sun Damfari Mutane Fiye Da Naira Miliyan 70

Rundunar ‘yan Sandan jihar Imo, ta damke wasu matasa uku, da suka shahara wajan damfarar mutane ta hanyar yanar gizo, inda suke yin shigar burtu da sunan shugaban ma’aikatan gidan Gwamnatin jihar ta Imo.

Kakakin ‘yan Sandan jihar Imo DSP Andrew Enweram,da yake nuna matasa ga ‘yan jarida, yace ‘yan damfaran sun bude wani shafi a dandalin sada zumunta na facebook, da suna Uche Nwosu, shugaban ma’aikatar gidan gwamnarin jihar Imo, da hotunan sa a bakin aiki.

Ganin wanna sai mutane suka dauka da shugaban ma’aikatar suke hulda inda aka yi batun filaye kwangiloli da batun Takin zamani da ma na daukar ma’aikata.

Matasan da ake zargi sun hada da Nwokoma Ezekach, Reuben Ogwuonye Ubongwung da Nwaeguzor Hope Miracle, wace ta kasance shugabar su.

Kakakin na ‘yan Sanda ya kara da cewa matasan sun damfari mutane fiye da Naira miliyan saba’in, yana mai cewa koda yake basu amsa laifin ba za a gurfanar dasu a gaban kuliya.