Wasu Mata ‘Yan Najeriya Sun Maida Martani Ga Zaben Amurka

Yayin da ake cigaba da bayyana ra’ayi game da sakamakon zaben kasar Amurka, kungiyoyin mata a Najeriya ciki har da lauyoyi sun maida martani da cewa akwai abin dubawa ga makomar siyasar mata.

Baya ga ‘yan siyasa suma kungiyoyin mata sun tofa albarkacin bakin game da zaben Amurka da aka gudanar har Donald Trump ya samu nasarar lashewa.

Malama a Kwalejin koyar aikin Shari’a ta jihar Adamawa Barista Nari Welye, tace bata ji dadin faduwar Hillary Clinton ba, amma ta yaba da kalaman ‘yar takarar jim kadan bayan da ta fadi zaben, haka kuma ta shawarci mata da su ci gaba da gwagwarmaya a siyasa.

A cewar wata ‘yar gwagwarmaya mai suna Mairo salmanu, bata ji dadin sakamakon zaben ba kasancewar Donald Trump mutum ne mai nuna gatse da jida kai, hakan yasa mutane suke tsorata. Ta kuma ce Amurkawa na fadadwa kasashe masu tasowa su zabi mata, amma sai gashi sunki zabar mace kwararriya da ta goge harhar gwamnati, sannan suka zabi Trump da bai taba rike ko mukamin gwamnati daya ba.

Yanzu haka dai ana jira domin ganin yadda sabuwar gwamnatin Amurka zata kaya.

Domin karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu Mata ‘Yan Najeriya Sun Maida Martani Ga Zaben Amurka - 2'15"