Wasu masana tattalin arziki sun bi sawun IMF akan karya darajar Nera

Takardan kudin Najeriya Nera

Yayinda ake cigaba da batun darajar Nera wasu masana tattalin arziki sun bi sawun hukumar bada lamuni ta duniya ko IMF akan lallai gwamnatin Najeriya ta karya darajar takardar kudinta

Wasu masana tattalin arziki a Najeriya sun bi sawun hukumar bada lamuni ta duni wato IMF wadda tuni ta kira gwamnatin kasar ta karya darajar kudinta Nera akan kudin dalar Amurka.

A wannan makon tsohon gwamnan babban bankin kasar Joseph Sanusi da wani masana tattalin arziki Farfasa Patrick Otomi sun kira gwamnatin Najeriya da ta karya kudin Nera.

Amma a wani hannun kuma mataimakin shugaban Najeriya Farfasa Yomi Osinbajo ya sake jaddada matsayin gwamnatinsu akan Nera. Yace gwamnatin su ta talakawa ce saboda haka ba zasu karya darajar kudin ba domin talaka ne zai kara tsundumawa cikin wahala.

Muryar Amurka ta tambayi wani masanin tattalin arziki Alhaji Kasumu Garba Kurfi akan abun dake haddasa faduwar darajar Nera. Yace abubuwa biyu ke haddasa faduwar darajar Nera. Abu na daya kasar bata sarafa komi sai ta shigo dashi daga kasar waje. Komi 'yan kasar zasu yi anfani dashi hatta abun wanke baki sai an shigo dashi duk da albarkatun kasar dake akwai da za'a iya anfani dasu.Kasar da ta rayu a irin wannan hali dole ta shiga damuwa. Abu na biyu shine babu abun da kasar ke sayarwa a waje sai mai wanda farashinsa ya fadi warwas. Dole Nera ta fadi sai lokacin da kasar ta fara sarafa kayan da take anfani dasu da kanta.

Alhaji Kurfi ya gargadi gwamnati ta daina tallafawa Nera. Yin hakan tamkar taimakawa mutane su dinga sayen kayan waje. Gwamnati ta bar Nera ta samar ma kanta matsayi. Hakan zai tilastawa mutane su dinga sayen kayan gida.

Dr Muhammad Dauda Kontagora masanin tattalin arziki kuma malami a Jami'ar Bayero dake Kano yace karya Nera akan dalar Amurka ba karamin illa zai haifarwa gwamnati ba da kuma 'yan kasa saboda Najeriya bata da abun da take sarafawa sai dai sayar da man fetur. Gwamnati ta bar Nera ta yiwa kanta hukunci.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu masana tattalin arziki sun bi sawun hukumar bada lamuni ta duniya akan karya darajar Nera