A wannan watan wa'adin cimma burin kawar da talauci, daya daga cikin burorin muradun wannan karni zai kare, ba tare da an samu biyan bukatar da aka yi bege ba.
A taron da ofishin muradun wannan karni ya shirya a Abujan Nigeria akan wannan shiri da Majalisar Dinkin Duniya ke kula da shi.
Karewa wannan shiri yasa za'a kafa wani shiri a watan gobe na Satumba idan Allah ya kaimu mai suna "SUSTAINABLE DEVELOPMENT GOALS: da turanci a Nigeria. Wannan shiri zai yi aiki har zuwa shekara 2030, kuma yana bukatar dala triliyan talatin domin samar da abubuwan more rayuwa.
Mansur Manu Soro mai bada shawara akan wannan shiri ya shedawa wakilin sashen Hausa Nasiru El Hikaya cewa masana sun yi kiyasin cewa akwai muradun da za'a sake gabatarwa guda goma sha bakwai.
Tuni har an yi taro akan yadda za'a gabatar ko kuma sanar da kudaden gudanar da wannan shiri. Ana bukatar makudan kudade domin kawar da matsanancin talauci a duniya. Ana kuma bukatar dala triliyan bakwai wajen samar da abubuwan more rayuwa.