Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faduwar farashin Mai a Kasuwanin Duniya


Wani gidan mai a Lagos.
Wani gidan mai a Lagos.

Kasashe maso dogoro akan mai, irinsu Nigeria, sai sun sake lale a saboda faduwar farashin mai a kasuwanin duniya.

Faduwar farashin mai a kasuwanin duniya na nuna kasashe maso dogoro akan mai irinsu Nigeria sai sun sake shiri, sun fito da hanyoyin cike gibin da hakan zai haifar a kasafin kudi da lamuran tattalin arziki.

Masana sun fara nuna muhimmancin fadada hanyoyin kudin shiga da suka hada da zuba jari a bangaren noma da ma'adinai.

Salihu Lukman masanin tatalin arziki. Yace a kauyuka da birane za'a ga mutane masu karfin jiki suna zaune, sai zaman kashe wando. Yace yadda ake gudanar da harkoki, bai sa an sa su a hanyar da za su je su amfana da kan su ba.

Mallam Salihu yace wannan shine baban illa a halin da Nigeria take ciki. Yace idan jihohi ba su je su karbi abin da aka ware musu daga gwamnatin taraiya ba, ba su da hanyar da zasu samo kudin shiga wanda zai sa su iya gudanar da harkokin gwamnati.

Yace kowa a Nigeria yana jira ne ya samu wani abu daga hannun gwamnati. Yace wannan hali shine ya kamata a canja.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG