Wasu Kasashe Uku Sun Amince Aika WakIlai Zaman Yarjejeniyar Siriya

Kasashen Rasha, da Turkiyya da Iran sun amince yau Talata su bada wakilai da za su sa ido akan yarjejeniyar tsagaita wuta a Siriyya, yayin da suka kawo karshen ganawar kwanaki biyu a Astana da jami’ai daga gwamnatin Siriyya da kuma ‘yan tawaye.

Kasashen 3 sun jaddada a wata sanarwar hadin gwiwa cewa yakin Siriyya da aka kwashe kusan shekaru 6 ana yi, amfani da karfin soja ba zai warware rikicin ba, amma ganawar neman sulhu karkashin ka’idodin MDD ita ce kadai mafita wajen samun zaman lafiya.

Haka kuma sun jaddada matsayarsu akan kin amincewa da kungiyar ISIS da ta Nusra Front.

Ana sa ran yin wani zagayen ganawar zaman lafiya ranar 8 ga watan Fabarairu a Geneva, karkashin jagorancin Jakadan Siriyya a MDD Staffan de Mistura.