Shugaban kuma ya dakatar da daukar ma’aikata a ma’aikatun gwamnatin tarayya, ya kuma jaddadawa shugabanna majalissar tarayyar kasar cewa kurakuren zabe ne suka hana shi samun kuri’un jama’a a zaben da aka yi a watan Nuwamba.
A wata ganawa da aka yi a fadar White House, wadda ta hada da shugaba majalissa Paul Ryan, da shugaban ‘yan majalissar rinjaye Mitch McConnell, da shugabar ‘yan jam’iyyar Democreta a majalissar wakilai Nancy Pelosi da da shugaban majalissar dokokin na jam’iyyar Democrat Chuck Schumer, mutane da yawa da suka san da wanna tattaunawar sun ce Trump yayi ikirarin cewa tsakanin kuri’u miliyan 3 zuwa miliyan 5 da aka yi magudinsu baki wadanda ba ‘yan kasa ba ne suka jefawa abokiyar takararsa Hillary Clinton
Ba a dai sami wasu hujjojin da suka nuna an yi magudi a zaben ba, kuma tabbas in ma akwai basu kai yawan haka ba.
Ms. Clinton ce ta sami galibin kuri’un da jama’a suka kada inda ta sami kuri’u miliyan 2. Trump ya sami nasarar zama shugaban kasa ne saboda ya sami kuri’u masi rinjaye daga wakilan zaben Amurka, wadanda ma kusan su ke zaben shugaban kasa.