Jiya a Fadar White House, Trump ya ce, "Wani mashahurin al'amari ne ga ma'aikaci a Amurka - abin da mu ka yi yanzun nan."
Sabon Shugaban na Amurka, kamar yadda takwarorin aikinsa na Republican su ka yi a baya, shi ma ya kafa dokar hana amfani da kudin gwamnati wajen daukar nauyin kungiyoyin kasa da kasa masu nasaba da rubar da ciki.
Baya ga haka, Trump, wajen cika alkawarin da ya yi lokacin yakin neman zabe, ya tsai da daukar ma'aikata a ma'aikatun gwamnatin tarayya da dama, a matsayin wani fannin rage kudaden da gwamnati ke kashewa.
Yarjajjeniyar cinakayyar da Amurka ta bari, tun a 2009 aka cimma a gwamnatin tsohon Shugaba Barack Obama, to amma Majalisar Tarayyar Amurka ba ta ida rattaba hannu a kanta ba, ganin yadda wasu mambobin Majalisar ke adawa ko dari-dari da yarjajjeniyar. Da an tabbatar da yarjajjeniyar da ta kunshi cinakayya da Japan da Australia da New Zealand da Malaysia da Chile da Canada da Mexico da kuma wasu kasashen hudu.
Mai maganda da yawun Fadar White House Sean Spicer, ya gaya ma 'yan jarida cewa, kamar yadda Trump ya yi ta fadi a baya, irin wanna yarjajjeniyar ta kasashe da dama ba ta kare muradunmu ba, kuma zai hanzarta daukar matakin yada manufofin cinakayyan da za su kara bai wa ba-Amurke ma'aikaci da kuma mai masana'anta damar yin fice.