A yau Litinin wasu karin jihohin Amurka sun shirya daukar matakan dage dokar takaita zirga-zirga da aka saka don dakile yaduwar annobar coronavirus, a yayin da jami’an kiwon lafiya na tarayya suka kara bayyana wasu alamu na kara yaduwar cutar.
Jami’an lafiya na Amurka sun ce jin-sanyi da makarkata, ciwon gabobi, ciwon kai, kaikayin makoshi, gushewar jin kanshi ko wari da rashin jin dan-dano duk suna iya zama daga cikin alamun cutar ta coronavirus.
A baya hukumar yaki da cututtuka ta Amurka CDC ta ce, alamun cutar sune zazzabi, karancin numfashi, da tari a matsayin alamun annobar ta COVID-19.
Shugabannin jihohin Colorado, Mississippi, Montana, da Tennessee sun bada damar ‘yan kasuwa su fara gudanar da harkokin su a yau Litinin. Sun bi sahun jihohin Georgia, Oklahoma, Alaska da South Carolina a yunkurin ganin mutane sun koma bakin aiki, da baiwa jama’a dama komawa rayuwar su da suka saba.
Kwararru a fannin kiwon lafiya na kara jan hankali akan gaggauta komawa bakin aiki, amma gwamnoni na cewar an dauki duk matakan da suka kamata don kare lafiyar jama’a.
Wadanda suka kamu da cutar sun kai mutum 980,000 a kasar da suka hada da mutum 55,000 da suka mutu.
Jihar New York ita ce cutar tafi kamari a Amurka da kashi kusan 30 cikin dari na baki dayan waddanda suka kamu a kasar.