Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba’a yake yi da ya ba da shawarar cewa za a iya amfani da maganin kashe kwayoyin cuta a matsayin maganin coronavirus.
Kalaman na Trump sun biyo bayan damuwa da kwararru da gargadin da kamfanonin da suke hada ruwan magungunan kashe cutar da ake kira “disinfectants” a turance suka yi kan amfani da magungunan.
A ranar Juma’a shugaban na Amurka ya ce kalaman da ya yi a ranar nan, bai yi su don a dauke su da muhimmanci ba.
“Kawai ina tambaya ne cikin ba’a ga manema labarai, domin na ga abin da zai faru,” in ji Trump.
Yayin taron manema labarai da ake yi a fadar gwamnati ta White House a ranar Alhamis, Trump ya ce ya kamata masana kimiyya su duba yiwuwar saka ruwan magungunan kashe cuta a jikin masu fama da cutar COVID-19.
Kalaman nasa dai sun janyo ka-ce-na-ce a sassan duniya.
Facebook Forum