Wasu Gwamnonin Najeriya Da Na Maradi Sun Tattauna Batun Tsaro

Maradi

Gwamnonin jahohi masu iyaka da Maradi ta jamhuruyar Nijar irin su Katsina da Zamfara da Sokoto da kuma Maradi sun gudanar da wata muhimmiyar ganawa a Maradi, inda suka tattauna game da matsalar tsaro da suke fama da ita a yankunan na su.

A kwanakin baya da 'yan bindiga suka addabi yankunan da hare-hare da sace-sacen mutane, shine dalilin da yasa al'ummar wannan yanki na Najeriya, yin gudun hijira zuwa Maradi, inda yanzu haka suke samun kulawa daga hukumomin jihar.

Gwamnonin sun tsaya akan zasu tuntubi wadannan mutane da sasantawa,
inji Aminu Wazira Tambuwal gwamnan jihar Sokoto, idan hakan bai samu ba
za suyi anfani da abin da ba a so, wato tsinin bindiga.

Shi ma ana shi bangaren gwamnan jihar Maradi Zakari Umaru, ya ce zasu
hada karfi da karfe tsakanin sojojin Nijar da na Najeriya, domin su tunkari
matsalar. Ya ce kuma game da 'yan gudun hijirar na Maradi gwamnonin na
Najeriya sun tabbatar musu da cewa da zarar sun koma gida, za su duba abin da ya dace a kwashe su, su koma garuruwan su.

Ana su bangaren 'yan gudun hijirar sunce wannan shine fatansu, na ganin an mayar da su garuruwansu na asali.

Saurari cikakken rahoton daga wakiliyar Muryar Amurka Tamar Abari.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnonin Katsina, Sokoto, Zamfara Da Maradi Sun Hallara A Nijar