Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dangantaka Ta Yi Tsami Tsakanin Najeriya Da Afirka Ta Kudu


Shoprite Najeriya
Shoprite Najeriya

‘Yan Najeriya na ci gaba da mayar da martani dangane da kisan da ake yiwa ‘yan kasar a can kasar Afirka ta kudu.

Yanzu haka dai ‘yan Najeriyar na bayyana mabanbantan ra’ayoyii da kuma matakai akan kamfanonin Afirka ta kudu dake aiki a Najeriya.

A jiya ne dai hukumomin Najeriya suka umarci jakadan kasar a Afrika ta kudu da ya koma gida, Inda su-ma mahukunta a Afrika ta kudun suka janye nasu jakadan a Najeriya.

Hakan dai na nuna, yadda alakar diplomasiyya ke kara tabarbarewa a tsakanin kasashen biyu.

A nasu bangaren, kamfanoni da cibiyoyin hada hadar kasuwanci mallakar kasar Afirka ta kudu a Najeriya kamar Kamfanin Sadarwa na MTN, da kantin Shoprite, na fuskantar kauracewar wasu abokan huldar ‘yan Najeriya.

Koda yake tun a shekaranjiya talata kamfanin MTN ya bada sanarwar rufe ofisoshin sa a sassan Najeriya bayan farmakin da wasu a jihar Legas suka kaiwa ofishini, amma kantin shoprite a Kano ya kasance a bude.

Ga cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Mahmud Ibrahim Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00



Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG